IQNA

An Canja Sunan Wani Masallaci Zuwa Masallacin Quds A Malaysia

16:52 - December 11, 2017
Lambar Labari: 3482189
Bangaren kasa da kasa, an canja sunan wani masallaci a kasar Malaysia zuwa masallacin Quds domin nuna rashin amincewa da kudirin Trump.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai nst cewa, Jamil Khair Behram minister mai kula da harkokin addini a Malaysia ya bayyana cewa, sun dauki wannan matakin ne domin ci gaba da nuna rashin amincewarsu da matakin Trump a kan birnin Quds.

Ya ci gaba da cewa sun kudiri aniyar saka wannan suna ne a kan babban masalalcin jahar Sokowan domin ci gaba da nuna goyon baya ga al'aummar Palastinu da kuma masallacin Quds mai alfarma.

Ministan na kasar Malaysia ya ce hakika matakin da shugaban Amurka ya dauka ya bata ran al'ummomi musulmi na duniya, kamar yadda al'ummar Malaysia ba a bar su a baya ba wajen nuna fushisu a kan haka.

Daga karshe yace za su ci gaba da bin dukkanin matakai da suka dace domin nuna rashin agamsuwa da wannan mataki na kure da shugaban Amurka ya dauka.

3671509

 

 

captcha