IQNA

Sarkin Musulmi Ya Yi Suka Kan Takura Ma Mata Saboda Saka Hijabi A Najeriya

16:55 - December 17, 2017
Lambar Labari: 3482208
Bangaren kas ada kasa, sarkin msuulmi a Najeriya ya yi kakausar suka dangane da yadda ake takura ma mata musulmi saboda saka hijabi.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na thebreakingtimes ya bayar da rahoton cewa, sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar a yain taron MPAC, ya bayyana abin da mata suke fuskata a kasar a wasu wurare saboda saka hijabi da cewa ya sabawa kaida.

Sarkin ya ci gaba da cewa, shi lullubi ban a musulmi ne kadai ba, tufafi ne na dukkanin addinai da aka saukar daga sama, da suka hada har da kiristanci da yahudanaci.

Haka nan kuma ya bayyana cewa, ya zama a karfafa batun sulhu da fahimtar juna a tsakanin dukkanin al'ummar kasa baki daya, tare da girmama juna da kuma girmama akidar kowa.

Ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi bayani dalla-dalla kan hakkokin al'umma na addini, saboda haka bai kamata musulmi a haramta musu wasu daga cikin nasu hakkokin na addini da kuma fahimtarsu ba.

Fiye da kasha 60 cikin dari na sama da mutane miliyan dari da tamanin da hudu da suke rayuwa a Najeriya dai musulmi ne.

3673448

 

 

 

 

captcha