Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wannan taro ya gudana ne a birnin Lagos babbar cibiyar kasuwanci ta tarayyar Najeriya, tare da halartar masana da kuma kungiyoyin kare hakkin musulmi.
Alhaji Laila Tala wani fitaccen dan jarida ne musulmi a Najeriya wanda ya gabatar da kasida a wajen taron, inda yake bayyana cewa hakika musulmi suna fuskantar rashin adalci daga wasu bangarori na sadarwa a kasar.
Inda ya bayyana cewa lamurra da dama suna wakana da musulmi a dukkanin yankuna na kasar, amma ba kasafai a kan bayar da rahoton yadda yake ba.
Ya ce musulmi babban bangare mai matukar muhimmanci a Najeriya, wanda dole ne a tafi da su,a kan haka yin adalci ga musulmia cikin dukkanin lamurra da suka shafe ko suka shafi addininsu wajibi ne.
Akintola shi ne shugaban kuniyar kare hakkin musulmi a Najeriya, ya gabatar da tasa kasidar, inda yake bayyana muhimamncin samun hadin kai da fahimtar juna a tsakanin musulmi da dukkanin bangarori a Najeriya.
Tarayyar Najeriya dai tana da mutane da suka kai miliyan 180 da suka hada da musulmi da kirista.