IQNA

Za A Bude Masallaci Mai Suna Masallacin Shahidan Rauda

16:47 - January 09, 2018
Lambar Labari: 3482281
Bangaren kas ada kasa, a cikin wannan makon mai kamawa ne za a bude wani masallaci mai sunan shahidan Rauda a garin Aswan da ke kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alfajr cewa, a cikin wannan makon mai kamawa ne za a bude wani masallaci mai sunan shahidan Rauda a garin Aswan da ke kasar Masar tare da halartar Muhammad Mukhtar Juma'a minister mai kula da harkokin addini na kasar.

Taron zai samu halartar masana da malamai musamman limaman Juma'a, inda za a gabatar da jawabi kan muhimmancin yin amfani da wuraren wa'azi domin jan hankulan matasa da ake rudarsu suna shiga kungiyoyin ta'addanci da sunan addini.

A cikin 'yan makonnin da suka gabata ne dai 'yan ta'adda masu dauke da akidar wahabiyanci suka kai hari kan masallata  alokacin sallar Juma'a, tare da kashe masallata 305 da kuma jikkata wasu da dama.

3680607

 

 

captcha