IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Kur'ani ta Khartum

15:53 - January 10, 2018
Lambar Labari: 3482284
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar kur'ani mai tsarki karo na tara da ake yi wa take da gasar Khartum a kasar Sudan.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, a jiya ne aka fara gudanar da gasar kur'ani mai tsarki karo na tara da ake yi wa take da gasar Khartum a hukumance kasar Sudan tare da halartar makaranta da mahardata 71 daga kasashen duniya.

Muhammad Rasul Takbiri shi ne yake wakiltar jamhuriyar musulunci ta Iran a wannan gasar, inda a daren jiya ya amsa tambayoyin da aka yi masa na share fagen shiga gasar gadan-gadan.

Daga cikin surorin da ya amsa tamabya  akansu akwai Al Imran, Hud da kuma Mujadalah.

Wannan gasa ana gudanar da ita a babban dakin taruka na birnin Khartum kamar yadda aka saba gudanarwa.

3680807

 

 

captcha