IQNA

Dan Sheikhul Mubtahilin A Kasar Masar Ya Rasu

16:18 - January 10, 2018
Lambar Labari: 3482286
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Ahmad Sayyid Naqshbandi dan Sayyid Muhammad Naqshbandi shugaban masu begen manzon Allah ya rasu yana da shekaru 77 a duniya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa ya nakalto daga shafin Almisriyun cewa, Sheikh Ahmad Sayyid Naqshbandi dan Sayyid Muhammad Naqshbandi shugaban masu begen manzon Allah ya rasu yana da shekaru 77 bayan fama da rashin lafiya.

Bayanin ya ce Sayyid Naqshbandi duk da cewa yana sauti mai kyau kamar na mahaifinsa, amma dai bai taka rawa kamar mahaifinsa wajen gudanar da ayyuka na bege ba.

Dubban mutane ne da suka hada da malamai da kuma makaranta kur'ani mai tsarki suka halarci janazar tasa a mahaifarsa da ke Tanta, kamar yadda dubban jama'ar gari suka halarci jazar wanann malami, wanda ya bayar da gudunmawa a fagen yada ilimin kur'ani.

A cikin shekara ta 1976 mahaifinsa Sayyid Muhammad ya rasu, wanda ake ye wa lakabi da shugaban masu bege na kasar Masar baki daya, wanda kuma tun bayan rasuwarsa aka mayar da lakabin a kan dansa.

3680703

 

 

 

captcha