IQNA

Jagoran Darikar Muridiyyah Ya Rasu A Kasaar Senegal

21:13 - January 11, 2018
Lambar Labari: 3482287
Bangaren kasa da kasa, Allah ya yi wa jagoran darikar Muridiyya Sheikgh Sarin Mukhtar Mbaki rasuwa a kasar Senegal yana da shekaru 94 a duniya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Allah ya yi wa jagoran darikar sufaye ta Muridiyya Sheikgh Sarin Mukhtar Mbaki rasuwa a kasar Senegal yana da shekaru 94 a daren jiya Laraba.

Malamin dai yana a matsayin jika ne gag a sheikh Amadou Bamba wanda ya assasa wannan darika ta Muridiyya, kuma ya rasu ne a garin Tuba babban birnin mabiya wannan darika a kasar ta Seneal, bayan fama da rashin lafiya da kuma tsufa.

Jim kadan bayan sanar da labarin rasuwarsa, gwamnatin kasar Senegal ta sanar da makoki na kasa baki daya.

An bizne wannan malami a wurin da ake bizne manyan malaman wannan darika a garin na Tuba.

3680984

 

 

 

captcha