IQNA

Kayan Tarihi Na Asia A Baje Kolin Kayan Addinai A A Okland

23:10 - January 12, 2018
Lambar Labari: 3482292
Bangaren kasa da kasa, an nuna wasu daga cikin kayan tarihi a yankin Asia a baje kolin kayan taihin addinai a jami’ar Carolina ta arewa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na dailytarhee wa, wannan shi ne karu na uku da ae gudanar da wannan baje a kowace shekara a wannan jami’a a bangaren adanawa da kuma binciken kayan tarihi.

Baje kolin dai ya shafi abubuwan da suka safi tarihin nahiyar Asia ne musamman ma wadanda suka safi addinai.

Babban jami’I mai kula da wannan baje koli ya bayyana cewa, nahiyar Asia tana da babban muhimmanci ta fuskar tarihi, kamar yadda kuma take da muhimmanci ta uskar addinai.

Dukkanin addinai daga aka sauka daga sama dai sun zo ne daga yankin Asia musamman ma a gabas ta tsakiya.

Baje kolin ya fara ne daga wanann wata, kuma zai ci gaba har nan zuwa watanni uku masu zuwa.

3681157

 

 

 

 

 

 

captcha