IQNA

Malamin Kirista Ya Bayar Da Kyautar Kur’ani Ga Wani Limami Musulmi

23:40 - January 13, 2018
Lambar Labari: 3482294
Bangaren kasa da kasa, wani malamin addinin kirista ya bayar da kyautar kwafin kur’ani mai tsarki a lokacin taron bude wni masallaci a lardin Sharqiyya a Masar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bawwaba News cewa, a jiya ne Khalid Said gwamnan lardin Shaqiyyqh ya jagoranci bude wani sabon masallacin Juma’a a lardin.

A yayin gudanar da bikin bude masallacin, wannan malamin adinin kirista ya mika kwain kur’ani mai tsarki ga limamin da zai rika jagorantar salla a wurin.

Baya ga haka kuma ya bayyana cewa, ya bayar da wannan kyauta mafi girma da kima ne domin kara tabbatar wa usulmi da kirsta cewa, mabiya wadannan addinai guda biyu ‘yan uwa ne dukkaninsu suna bin addinai ne da aka saukar daga sama.

Kuma za su ci gaba da kasancewa tare suna masu girmama juna da fahimtar juna, ayyukan wasu jahilai daga cikinsu ba zai hada su ba, domin kuwa musulunci da kiristanci dukkaninsu suna kira zuwa ga zaman lafiya da girmama dan adam da kuma girmama fahimtarsa.

Masallacin wanda aka bude a garin Zaqayik da ke cikin lardin Sharqiyya yana da fadin mita murabbai 220, kuma zai dauki masallata kimanin 350 a cikin gininsa.

3681397

 

 

 

captcha