IQNA

Jahar Bauchi A Najeriya Ta ware Kasafin Kudi Domin Gasar Kur’ani

21:54 - January 14, 2018
Lambar Labari: 3482298
Bangaren kasa da kasa, jahar Bauchi da ke Najeriya ta ware wani kasafin kudi mai yawa da ya kai Naira miliyan 53 domin tallafawa gasar kur’ani mai tsarkia  jahar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya naklato daga shafin jaridar Daily Trust cewa, Zubairu Madaki shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin gasar kur’ani na jahar, ya bayyana cewa an ware na miliyan 17 domin sayen mota da kuma wasu abubuwan bayarwa  a matsayin kyauta ga wadanda suka nuna kwazo a gasar.

Ya ci gaba da cewa suna shirin gasar kur’ani ta kasa da za a gudanar ta shekarar 2018 a jahar Katsina.

Haka nan kuma ya kara da cewa gasar jahar Bauchi ta samu halartar makaranta da mahardata 225 da suka hada da maza 115 da kuma mata 105 daga yankuna 20 na jahar.

Ya kara da cewa babbar manufar gasar ita ce kara zama cikin shiri domin zuwa gasar kasa baki daya, inda za a fitar da wadanda za su wailci jahar.

3681771

 

 

 

 

captcha