IQNA

Bam Ya Tashi Da Wani Kusa Na Kungiyar Hamas

21:56 - January 14, 2018
Lambar Labari: 3482299
Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga Lebanon na cewa dazun nan ne bom din ya tashi a cikin motar jami'in na Hamas, Muhammad Hamdan.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Tuni jami'an tsaron lebanon suka killace yankin da lamarin ya faru domin gudanar da bincikice.

Kawo ya zuwa yanzu babu cikakken bayani akan wanda ya kai wannan harin, sai dai 'yan gwagwarmaya a yankin sun fara nuna wa haramtacciyar Isra'ila hannun tuhuma.

A shekarun bayan dai, haramtacciyar Kasar Isra'ila ta sha kai hare-haren kisan gilla akan 'yan gwgawarmayar palasdinu da kuma na Hizbullah a cikin kasar ta Lebanon.

Sheikh Maher Hammud babban limamin Juma’a na garin saida kuma shugaban gayammar malaman gwagwarmaya na duniya ya zargi haramtacciyar kasar yahudawa da ma’aikatanta da aikata wannan danyen aiki.

3681916

 

 

captcha