IQNA

Jami'an Tsaron Libya Sun Kame Wani Mai Safarar 'Yan Ta'addan Daesh

16:53 - January 15, 2018
Lambar Labari: 3482301
Bangaren kasa da kasa, jami'an tsaro a kasar Libya sun kame wani mutum yana safarar mayakan 'yan ta'adda na Daesh.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran sporting ya habarta cewa, jami'an tsaro sun kame wani mutum mai safarar yan ta'addanci Daesh a yankin Buhadi a cikin gundumar Sirte.

Bayan kame mutumin ya tabbatar da cewa yana yin hanya ne ga 'yan ta'addan Daesh daga yankunan da suke boye a cikin yankunan da ke gundumar Sirte a gabashin Libya zuwa yankunan kudancin kasar.

A cikin shekarar da ta gabata ce jami'an tsaron kasar Libya suka sanar da kammala tsarkake birnin Sire da kewaye daga 'yan ta'addan wahabiya na Daesh.

A cikin shekarar dubu biyu da sha biyar 'yan ta'addan wahabiya na Daesh suka kwace iko da birnin Sirte mahaifar tsohon jagoran kasar.

Kasashen yammacin turai da kuam wasu daga cikin larabawa ne dai suke daukar nauyin 'yan ta'adda a kasar Libya, wadanda suka tarwatsa kasar bayan kisan gillar da suka yi wa tsohon jagoran kasar.

3682147

 

 

 

 

 

captcha