IQNA

Dan Majalisar Dokokin Ghana Ya Yaba Da Hikimar jagoran Juyin Muslunci

20:15 - January 16, 2018
Lambar Labari: 3482303
Bangaren kasa da kasa, dan majalisar dokokin kasar Ghana dake wakiltar yankin arewacin kasar ya yaba da irin hikimar da jagoran juyin juya halin muslunci na Iran wajen kokarin hada kan al’ummar musulmi.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na cibiyar yada al’adun muslunci cewa, Malik Abdullahi dan majalisar dokokin kasar Ghana dake wakiltar yankin arewacin kasar ya yaba da irin hikimar da jagoran juyin juya halin muslunci na Iran wajen kokarin hada kan al’ummar musulmi na duniya baki daya.

Ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da shugaban ofishin yada al’adu na Iran da ke kasar Ghana Muhammad Hasan Ipekchi a jiya.

Dan majalisar na Ghana ya ce ya halarci taron hadin kan musulmi da aka gudana a Iran a cikin watan maulidi da ya gabata, kuma ya hakarci taron ganawa da jagora a gidansa, inda suka saurari bayanin da yayi musu kan muhimmancin hadin kan al’ummar musulmi.

Ya ce ko shakka ya tasirantu matuka da wadannan kalamai, domin bai

taba jin irin haka daga wani jagoran addini a kasashen muuslmi ba.

Kamar yadda kuma ya bayyana cewa idan da dukkanin musulmi za su ajiye duk wani batun banbanci da bangaranci da ke hana su hada kai, to da babu wanda ya isa nuna su da yatsa a duniya.

To amma abin ban takaicin a cewasa shi ne, yadda wasu daga cikin shugabanni da sarakuna na kasashen msuulmi suka zama  asahun gaba wajen kare manufofin kasashen da suke kiyayya da musulunci, abu mafi muni ma da sune ake kokarin rusa kasashen musulmi da haifar da fititunu da yake-yake a cikin su.

3682596

 

 

captcha