IQNA

Wasikar Isma’il Haniya Zuwa Ga Jagora:

Al’ummar Palastine Suna Jinjina Wa Iran Kan Taimakon Da Take Yi Musu

23:33 - January 18, 2018
Lambar Labari: 3482312
Bangaren siyasa, Isma'ila Haniya Shugaban kungiyar HAMAS wacce take gwagwarmaya da haramtacciyar gwamnatin Isra'ila da makami ya rubutawa jagoran juyin juya halin musulunci Ayatollah Sayyid Aliyul Khamenei wasika inda yake yabawa kasar iran da irin goyon bayan da take bawa al-ummar Palasdinu.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shugaban na Hamas ya godewa jagoran kan nasihohin da yake yi wa kungiyar. Ya kuma kara da cewa manufar gwamnatin Amurka da haramtacciyar kasar Isara'ila na shelanta Qudus a matsayin cibiyar gwamnatin Isar'ila ita ce kwance damarar kungiyar ta Hasam sannan bayan haka maida huldan jakadanci a fili tsakanin Isar'ila da kasashen larabawa.

A wani bangare na wasikarsa Isma'ila Haniya ya bayyana cewa gwagwarmayar Intifada ce kadai, da yardar Allah zata kawo karshen mummunar manufofin kasashen Amurka da magoya bayanta a yankin.

Kasar Iran dai ita ce kasar da take taimaka ma al’ummar Palastinu da kudade da kuma ta fuskar soji da kuma hatta  wasu kayan bukatar rayuwa, kamar yadda ta taimaka msu wajen sake gina gidajensu da Ira’ila ta rusa.

Kasashe masu girman kai na duniya suna bayyana batun matsayar Iran dangane da Isra’ila da kuma taimakon da take baiwa palastinawa a matsayin babbar matsalarsu da ita, kuma dukkanin matsalolin da kasashen yammacin turai suka saka Iran a ciki yana da alaka da haka ne.

Haniyya ya bayyana taimakon da Iran take baiwa hamas da sauran kungiyoyin Palastinawa a matsayin babban abin da yasa har yanzu suke ci gaba da wanzuwa a matsayin kungiyoyin gwagwarmaya da suke kare al'ummar palastine gwagwardon karfinsu, wanda da ba don taimakon Allah da Iran ba, da tuni sun zama labari.

3683108

 

captcha