IQNA

Gasar Zaben Kyawawan Sautukan Karatun Kur’ani A Masar

23:33 - January 19, 2018
Lambar Labari: 3482313
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar za ta shirya gudanar da gasar zaben mutane masu kyakyawan sautin karatun kur’ani.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Muhammad Mukhtar Juma’a ministan ma’aikatar kula da harkokin adini a kasar Masar ya bayyana cewa, za a shirya gudanar da gasar zaben mutane masu kyakyawan sautin karatun kur’ani ta kasa baki daya.

Ya ci gaba da cewa, wannan gasa tana da matukar muhimamnci, domin kuwa ta haka ne za a fitar da mutane da suke da kyawawan sautin karatun kur’ani da kuma begen manzon Allah wadanda za su rika bayyana gidajen talabijin da radio da kuma wuraren taruka gami da masallatai.

Daga karshe ya zuwa yanzu kofa bude take ga duk wani mutum dan kasar Masar da yake son shiga gasar da ya aiko da sautinsa na tsawon mintuna uku ta hanyar yanar gizo a shafin da ma’aikatar addinai ta bude domin gasar.

3683351

 

 

captcha