IQNA

Malamin Jami’ar Cambriege Ya Ce Fahimtar Kur’ani Na Tattare Da Ci Gaban Dan Adam

23:37 - January 26, 2018
Lambar Labari: 3482337
Bangaren kasa da kasa, Muiz Masud malami ne a jami’ar Cambriege da ke kasar Birtaniya wanda ya gabatar da jawabi a gaban taron tattalin arziki a birnin Davos na kasar Switzerland.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar yaum sabi ta bayar da rahoton cewa, Muiz Masud malami ne a jami’ar Cambriege da ke kasar Birtaniya, a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban taron tattalin arziki a birnin Davos na kasar Switzerland, ya bayyana cewa addinin mulsunci ya zo ma dan adam da gagarumin ci gaba.

Ya ce kur’ani mai tsarki shi ne littafin da addinin muslunci ya zo da shi, wanda kuma  acikin ya kunshi dukkanin naui na ci gaban dan adam da gyara rayuwarsa ta zamantakewa da kuma samun kyakyawan rabo bayan mutuwa.

Dangane da yadda muslunci yake kallon ci gaba ta fuskar tattalin arziki, kur’ani mai tsarki ya fayyace yadda ya kamata a tafiyar da dukiya da kuma tallafawa marassa karfi a cikin al’umma, ta yadda masu dukiya za su amfana shi ma talaka ya amfana.

Baya ga haka kuma akwai tsare-tsare da dama wadanda suka danganci tafiyarwa a bangaren siyasa da kuma zamntakewa da tsaro, wanda dukkaninsu abubuwa ne da dan adam yake bukatar tsari a kansu.

Taron tattalin arziki na Davos dai an fara shi ne tun a cikin shekara ta 1972, domin halartar shugabanni da masana harkokin tattalin arziki na duniya, domin tattauna hanyoyin da za  abunkasa ci gaban tattalin arzikin kasashen duniya.

3685414

 

captcha