IQNA

Allah Ya Yi Wa Daya Daga Cikin Manyan malaman Kur’ani A Kasa Aljeriya Rasuwa

23:22 - February 12, 2018
Lambar Labari: 3482388
Bangaen kasa da kasa, Hajj Muhammad Dabbagi daya daga cikin manyan malaman kur’ani a kasa Aljeriya ya yi masa rasuwa yana da shekaru 84 a duniya.

Allah Ya Yi Wa Daya Daga Cikin Manyan malaman Kur’ani A Kasa Aljeriya RasuwaKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Al-sama na kasar Ajeriya ya habarta cewa, Sheikh Muhammd Dabbagi ya rasu ne a ranar Asabar da ta gabata, a garin haihuwarsa Tanarkuk, da ke cikin lardin Adrar.

An haifi sheikh Muhammada  cikin sekara ta 1934, sa’annan kuma ya shiga babbar makarantar kur’ani da ke fitar da malamai ta kasar a cikin shkara ta 1951.

A karshen shekara ta 1963 ya yi karatu a wajen babban malamin kur’ani na kasar a wancan lokacin sheikh Blkabir. Haka nan kuma a cikin shekara ta 1964 ya koma garinsu, inda ya bude makarantarsa ta farko.

Allah Ya Yi Wa Daya Daga Cikin Manyan malaman Kur’ani A Kasa Aljeriya RasuwaShehin malamin ya kasance daya daga cikin manyan malaman kur’ani da suka kafa mayan cibiyoyi da makarantu na ilimi musamman a bangaren ilimin kur’ani.

Haka nan kuma malamin ya kasance daya daga cikin manayan malaman darikun sufaye a kasar ta Aljeriya, da suka horar da mutane da dama a kan tafarkin sufanci da tsarkake zuciya da zikin Allah.

Baya ga koyarwa, malamin ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen hada kan al’ummar kasar Aljeriya da sulhunta kabilu da basu ga maciji da juna.

3690803

 
captcha