IQNA

Jami’an Tsaron Tunis Sun Cafke Wasu ‘Yan Ta’adda 5

23:30 - February 12, 2018
Lambar Labari: 3482390
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar harkokin cikin gida a Tunisia ta sanar da kame wasu ‘yan ta’adda masu maukar hadari su 5 a garin Dar Dima da ke cikin gundumar Jandawiyyah.

 

Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran ina ya habarta cewa, a jiya ma’aikatar harkokin cikin gida a Tunisia ta sanar da cewa jami’an tsaron kasar sun kame wasu ‘yan ta’adda masu maukar hatsari a garin Dar Dima da ke cikin gundumar Jandawiyyah a yammacin kasar.

Bayanin ya ce mutanen an kame su ne bayan samun wasu bayanan sirri dangane da wani shiri da suke da shin a kaddamar da wasu hare-haren ta’addanci a wasu yankunan kasar, kamar yadda kuma aka same su da hannu a wasu hare-haren da aka kai a lokutan baya.

Garin Dar Dima dai yana cikin lardin Jandawiyyah daya daga cikin larduna 24 na kasar Tunisia.

3690893

 

 

captcha