IQNA

Kuwait Ta Jinjina Wa Iran Wajen Taimaka Wa Iraki A Bangaren Tattalin Arziki

20:55 - February 15, 2018
Lambar Labari: 3482397
Bangaren kasa da kasa, Sarkin kasar Kuwait ya jinjina wa kasar Iran dangane da rawar da take bunkasa alakar tattalin arziki da Iraki, inda ya ce wannan na da matukar muhimmanci wajen habbaka tattalin arzikin kasar ta Iraki.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, Sarkin Kuwait Sabah Al-Ahmad AlJaber Al-Sabah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da ministan harkokin wajen kasar Iran Dr. Muhammad Jawad Zarif, bayan kammala taron tallafawa kasar Iraki da aka gudanar a jiya a kasar ta Kuwait.

A nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar ta Iran Muhammad Jawad zarif ya bayyana cewa, wajibi ne kasashen yankin sun warware duk wani sabani da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna, domin samun ci gaba da wanzuwar zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya baki daya.

Zarif ya ce Iran tana yaba wa kokarin da sarkin Kuwait ke yi na ganin ya shiga tsakanin kasashe da basa ga maciji da juna a yankin, domin samun sulhu a tsakaninsu.

Bangarorin Iran da Kuwait sun jaddada wajabcin kara bunkasa alakar da ke tsakaninsu ta fuskoki daban-daban, musamman a bangarorin kasuwanci, da harkokin bankuna na kasashen biyu.

3691761

 

captcha