IQNA

Jaddada Wajabcin Samar Da Hanyoyin Yaki Da Tsatsauran Ra'ayi A Taron Mauritania

22:40 - February 23, 2018
Lambar Labari: 3482422
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman taron kara wa juna sani na kafofin sadarwa da nufin samar da hanyoyin yaki da tsatsauran ra'ayi a yammacin Afirka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran gwamnatin Mauritania cewa, an gudanar da zaman taron kara wa juna sani na kafofin sadarwa da nufin samar da hanyoyin yaki da tsatsauran ra'ayi a yammacin Afirka, wanda aka gudanar a birnin Nuwakshout fadar mulkin Mauritania.

Babbar manufar taron dai ita ce yada sahihiyar fahimtar addini ta gaskiya a tsakanin musulmi da ma wadanda ba musulmi ba, domin kawar da karkataccen tunani na addini da ke kai wasu shiga ayyukan ta'addanci.

Daya daga cikin matsalolin da ake fuskanta a kasashen musulmi ita ce, mafi yawan mutane ba su san addinin ba, saboda haka sun dogara ne kawai da abin da wasu suka gaya musu a matsayin cewa shi ne addini, kuma suna karbar hakan saboda yardar da suka yi da irin wadannan mutane, wadanda sau tari su ne suke halakar da matasa tare da juya musu tunani da sunan addini.

Wannan taro ya cimma matsaya kan cewa malamai da limamai za su ci gaba da wayar da kan jama'a domin nisantar duk wata akida ta ta'addanci da kafirta musulmi.

3693867  

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha