IQNA

Hizbullah Ta Yi Kakkausar Suka A Kan masu daukar nauyin ‘Yan Ta’adda A Syria

22:39 - February 24, 2018
Lambar Labari: 3482425
Bangaren kasa da kasa, mamba a majalisar shawara ta kungiyar Hizbullah Sheikh Nabil Qawuq ya bayyana shiru da kasashen duniya suka yi kan ‘yan ta’adda ya bayyana irin goyon bayan da ‘yan ta’adda suke samu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran SANA na kasar Syria cewa, sheikh Nabil Qawuq mamba a majalisar shawara ta kungiyar Hizbullah ya bayyana shiru da kasashen duniya da na larabawa suka yi kan ta’addancin da ‘yan ta’addan wahabiyawan takfiriyya suke aikatawa  a Syria, ya bayyana irin goyon bayan da ‘yan ta’adda suke samu daga wadannan kasashe.

Ya ce ko shakka babu a duk lokacin da kasashen duniya masu girman kai na yahudawa suke son cimma wani buri a kan Syria ko kawayenta, sukan yi amfani da karnukan farautarsu daga cikin larabawa domin kara karfafa ‘yan ta’adda da makamai da kuaden man fetur da suke sayarwa, domin zafafa hare-hare a kan biranen Syria, domin yin amfani da hakan wajen cimma wani burin a siyasa  akan gwamnatin Syria ko kuma kawayenta.

3694085

 

 

 

 

captcha