IQNA

Birnin Vienna Zai Dauki Nauyin Bakuncin Tattaunawa Tsakanin Mabiya Addinai

22:43 - February 24, 2018
Lambar Labari: 3482426
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da zaman tattaunawa tsakanin mabiya addinai karo na biyu a matsayi na duniya a birnin Vienna fadar mulkin kasar Austria.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto dag shafin sadarwa na yanar gizo na INA cewa, a cikin wannan makon ne za a gudanar da zaman tattaunawa tsakanin mabiya addinai karo na biyu a matsayi na duniya a birnin Vienna.

Taron dai zai samu halartar masana daga sassa na duniya da suka hada da musulmi da wadanda ba musulmi ba, kamar yadda kuma wasu daga cikin ‘yan siyasa da jami’ai daga kasashen musulmi da na larabawa da turai duk za su halarci zaman taron.

Wannan taro dai na hadin gwiwa ne tsakanin cibiyar yada al’adu ta duniya da kuma cibiyar kula da harkokin jami’oi na kasashen duniya, wanda kungiyar raya al’adu da ilimi ta kasashen musulmi ISESCO ta dauki nauyin shirya taron.

Muhimman abubuwan da taron zai mayar da hankali a kansu sun hada da batun samar da yanayi na fahimtar juna da kuma girmama ra’ayin kow na akida, da karfafa zaman lafiya a tsakanin dukkanin mabiya addinai, da kuma yin watsi da duk wani bangare daga kowane addini wanda ya rungumi akidar ta’addanci da sunan addini.

3693990

 

 

captcha