IQNA

Taron Karawa Juna Sani Kan Tsarin Harkokin Kudi A Musulunci A Kasar Ghana

21:38 - March 11, 2018
Lambar Labari: 3482466
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani taron karawa juna sani harkokin kudi a mahangar addinin musulunci a kasar Ghana.

Taron Karawa Juna Sani Kan Tsarin Harkokin Kudi A Musulunci A Kasar GhanaKamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa ya nakalto daga shafin bangaren hulda da jama'a na jami'ar Ghana da ke birnin Acra cewa, a ranar Laraba mai zuwa za a fara gudanar da wani taron karawa juna sani harkokin kudi a mahangar addinin musulunci, wanda zai gudana a babban dakin taruka na jami'ar.

Abdul nashiru Isa Haku tsohon babban gwamnan bankin kasar Ghana tare da wasu daga cikin manyan jami'ai  bangaren harkokin tattalin arziki da hada-hadar kudade na kasar da kuam wasu daga jami'ar za su halarci taron.

Baya ga haka kuma Alhasan Andani babban daraktan Stanbic Bank zai gabatar da jawabia  wurin taron kan tsaron da musulunci yake da shi ta fuskar harkokin kudade da saka hannayen jari.

Nan da watanni biyu masu zuwa ne aka sa ran za a gudanar da wani babban taro kan bankin muslunci a kasar Ghana, wanda zai samu halartar masana daga kasashe daban-daban na duniya.

3698955

http://iqna.ir/fa/news/3698955

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna
captcha