IQNA

An Hana Limaman masallatai Fitar Da Fatawoyi A Kasar Aljeriya

21:42 - March 11, 2018
Lambar Labari: 3482467
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Aljeriya ta kafa dokar hana limaman masallatai fitar da fatawoyi a kasar.

Kamfanin dillancin labara iqna ya habarta cewa, jaridar yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, Muhammad Isa minister mai kula da harkokin addini a kasar Aljeriya ya bayyana cewa, sakamakon yadda ake samun fatawoyi masu jawo rashin fahimta tsakanin al'umma, an kafa dokar hana limaman masallatai bayar da fatawa  afadin kasar.

Ya ce wannan mataki ya zo ne sakamakon yadda wasu masu akidar tsatsauran ra'ayi suke fitar da fatawoyi tare da kafirta musulmi da suke da sabanin fahimta da su, wanda hakan ya sabawa koyarwar musulunci, kuma ya sabawa tsarin doka na kasar.

Akasrin mutanen kasar Aljeriya dai masu bin tafarkin darikun sufaye ne, amma daga bisani an fara samun masu dauke da akidar wahabiyanci da ke jawo rikici da rigingimu a tsakanin musulmin kasar, wanda hakan ya sanya ma'aikatar kula da addini ta kasar daukar wannan mataki, da nufin yin tsari na musamman wajen karbar fatawa a kasar.

 

3698771

 

 

 

 

captcha