IQNA

Musulunci Zai Zama Addini Mafi Girma A Duniya A Shekarar 2070

19:54 - March 14, 2018
Lambar Labari: 3482473
Bangaren kasa da kasa, wata cibiyar bincike da hasashe a kasar Amurka ta bayyana cewa addinin muslunci zai zama addini mafi girma a duniya daga zuwa 2070.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, cibiyar bincike da hasashe ta kasar Amurka pew ta sanar a cikin wani bayani cewa, bisa bincike mai zurfi da ta gudanar, ta iya yin hasashen cewa addinin muslunci zai zama shi ne addini mafi girma a duniya a cikin shekara ta 2070.

Sakamakon bincike ya nuna cewa, addinin muslunci shi ne addinin da yafi saurin yaduwa ta hanyar akida, kamar yadda kuma mabiyansa suke karuwa haihuwa fiye da sauran mabiya addinai.

Bayanin ya ce karuwar musulmi a tsakanin shekarun 2010 zuwa 20150, za ta kai kasha 73 cikin dari, yayin da karuwar kiristoci za ta kai kasha 35 cikin dari ne kawai.

Haka nan kuma sakamakon binciken ya nuna cewa a cikin shekara ta 2050, adadin musulmi zai kai biliyan 2.76, yayin da adadin kiristoci zai kai biliyan 2.92, wanda hakan ke nuni da bayan shekaru ashirin, adadin musulmi zai wuce na kiristoci a duniya.

Cibiyar PEW dai tana da babban mazauninta ne a birnin Washington na Amurka, kuma tana gudanar da bincike mai zurfi kan lamurra da dama, da kuma fitar da kididdiga.

3699778

 

 

 

captcha