IQNA

An Kawo Karshen Gasar Kur'ani Ta Kasa Da Kasa A Masar

16:22 - March 21, 2018
Lambar Labari: 3482496
Bangaren kasa da kasa, A yau ne ake kawo karshen gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a kasar Masar da aka gudanar a gundumar Portsaid.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ana gudanar da taron kammala gasar a yau a birnin Portsaid na kasar Masar, tare da halartar manyan jami'an gwamnatin kasar ta Masar da kuma baki daga kasashen ketare.

An gudanar da gasar tsawon kwanaki biyar, kuma a yau ne za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo a dukkanin bangarorin da aka gudanar da gasar.

Adel Gadban gwamnan lardin Portsaid ya bayyana cewa, hakika yin riko da kur'ani da al'ummar masar suke yi, shi ne babban sirrin samun nasarori da suke yi a dukkanin bangarori na rayuwa da ci gaban ilimi.

3701590

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha