IQNA

Akalla Mutane Uku Ne Suka Mutu A Harin Kasar Faransa

23:30 - March 23, 2018
Lambar Labari: 3482504
Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga kasar Faransa na cewa akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu sakamakon garkuwa da wani dan bindiga ya yi da mutane a garin Trebes.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Reauters cewa, mutumin da ya aikata wannan lamari ya kasha wani mutum a kusa da garin Trebes, kuma ya sace motarsa ya gudu.

Mutumin wanda ya bayyana kansa a matayin dan kungiyar ta’addanci ta Daesh, ya yi garkuwa da mutane a wani dakin cin abinci, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwa mutane biyu a wurin.

Emanuel Macron ya bayyana lamarin da cewa aiki ne na ta’addanci kuma yana da matukar hadari.

Daga bisani jami’an ‘yan sanda sun kashe mutumin tare da kubutar da mutanen da ya yi garkuwa da su.

Mutumin dai ya bukaci da a saki Salah Abdulsalam, mutumin da ake zargi da kai harin birnin Paris a cikin sekara ta 2015, wanda za a fara shari’arsa nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.

3701796

 

 

captcha