IQNA

Paparoma Ya Jinjina wa Shugaban Mabiya Mazhabar Shi'a Na Nahiyar Turai

23:47 - March 29, 2018
Lambar Labari: 3482523
Bangaren kasa da kasa, shugaban mabiya addinin kirista na darikar katolika Paparoma Francis ya jinjina wa shugaban mabiya mazhabar shi'a a nahiyar turai Ayatollah Ramedhani

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin jawabin sakon wata wasika da babban malamin ya aike wa Paparoma a farkon shekarar miladiyya, ya bayyana cewa:

 

Mai Girma Ayatollah Dr. Ramedhani

Pop Francis ya samu wasikarku, kuam yayi farin ciki matuka da kokarinku na ganin an samu fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiya addinai, da zaman lafiya mai dorewa.

A hakikanin gaskiya koyarwar addinai da aka saukar daga sama ita ce aminci da sulhu tausayi da taimako da fahimtar juna da girma juna da kuma mutunta dana dam, da tausayin mai rauni da kuma taimaka masa, kuma wasikarku ta kara tabbatar da hakan, kamar yadda Isa Almasihu ya koyar da 'yan adam cewa; kada mu karkata ga duniya da abin da ke cikinta mai karewa, mu koma zuwa ga gaskiya da hakika, mu rungumi ubangiji da maida hankali ga sha'aninsa.

Pop Francis na yi muku fatan samun dace da kariyar ubangiji da kuma samun taimakonsa, da fatan sulhu da amince a gare ku da ma mutanen duniya baki daya.

Fatar alhairi da gaisuwa a gare ku

Wanda ya fitar da sako

Mataimakin ministan harkokin waje

3702317

 

captcha