IQNA

Bahram Qasemi:

Neman Matsayi A Wurin Yahudawa Ya Sanya Yariman Saudiya Ya Wuce Gona Da Iri

18:50 - April 06, 2018
Lambar Labari: 3482544
Bangaren kasa da kasa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, a hankoron da yahudawa da makiya muslucni suke yi na neman kawo fitina da rarraba a tsakanin musulmi a halin yanzu sun samu wadanda suke bukata domin yi musu wannan aiki.

 Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Bahram Qasemi kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran a cikin wani bayaninsa da ya fitar a yau Juma'a ya bayyana cewa, a hankoron da yahudawa da makiya muslucni suke yi na neman kawo fitina da rarraba a tsakanin musulmi a halin yanzu sun samu wadanda suke bukata domin yi musu wannan aiki kyauta daga cikin larabawa.

Qasemi ya ce irin maganganu na wawanci da kuruciya da neman suna ko matsayi a wajen Amurka da yahudawa da yariman Saudiyya ya yi a zantawarsa da mujallar Time ta Amurka, ya tabbatar da cewa shi ya mika wuya kaci kaf ne ga manufofin makiya muslunci da al'ummar larabawa, ba tare da wani kwane-kwane kamar mahukuntan da suka gabace shi suke yi ba.

Ya ci gaba da cewa, ko shakka babu makiya addinin muslunci za su yi amfani da wannan matashi da suka dora a kan kujerar yarima mai jiran gado na kasar saudiyya, domin rusa ita kanta kasar ta Saudiyya da kuma sauran kasashen larabawa na yanakin gabas tsakiya.

Haka nan kuma ya yi ishara da yadda wannan matashi yake cin karensa babu babbaka a cikin masarautar Al saud ba tare da wani ya isa ya taka masa birki ba, wanda hakan ke tabbatar da cewa goyon bayan da yake takama da shin a iyayen gidan Alu Saud ne baki daya daga fadar white house da kuma manyan kungiyoyin yahudawa na duniya.

Qasemi ya ce zuwan wannan matashi mai fama da kuruciya da jahilci na  sanin inda rayuwa ta nufa balantana siyasar duniya a kan mulkin saudiyya, zai jefa musulmi da larabawa cikin babbar musiba.

3703406

 

captcha