Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a ci gaba da jerin gwano da gangamin da Palastinawa suka fara tun Juma'ar da ta gabata, a yau ma sun ci gaba da gudanar da gangami a yankin Zirin Gaza da sauran yankunan Palastinu.
Wannan gangami dai yana samun halartar dubban palastinawa daga kowane bangare da hakan ya hada da yankin zirin gaza da kuma yankunan gabar yamma da kogin Jordan da Quds.
Ko da jijjifin safiyar yau sojojin yahudawan Isra'ila sun kasha wasu palastinawa biyu a kusa da shingen da suka kafa tsakanin zirin Gaza da yankunan palastinwa da suka mamaye.
A ranar Asabar ce kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya zauna domin yin Allawadai da wannan mummunan aiki na yahudawan sahyuniya a kan al'ummar zirin Gaza bayan kisan mutane sha bakwai a rana guda, amma Amurka ta yi fatali da hakan.