IQNA

Zargin Dakarun Syria Da Kai Hari Da Makamai Masu Guba Ba Magana Ce Ta Hankali Ba

23:36 - April 08, 2018
Lambar Labari: 3482549
Bangaren kasa da kasa, kakain ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana zargin da Amurka ta yi wa dakarun Syria da kai hari da makamai masu guba a Doma da cewa ba Magana ce ta hankali ba.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wani bayani da ya yi yau, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi ya bayyana cewa; kasar Iran bisa akida ta addini da kuma sanin ya kamata a dabi'a ta dan adam ba ta yarda da yin amfani da makamai masu guba kan dana dam ba, kuma tana yin Allawadai da hakan, musamman ma ganin cewa ita kanta ta fuskanci wannan matsala ta san yadda take.

Qasemi ya ce; zargin da Amurka ta yi kan cewa sojojin Syria sun yi amfani da makamai masu guba a Douma da ke gabashin Ghouta a kan 'yan ta'adda da suka yi saura a wurin Magana ce maras kan gando wadda ta yi hannun riga da abin da yake a kasa.

Ya ce dalili na farko shi ne, a halin yanzu sojojin Syria su  ne suke da karfi kuam suke samun galaba a kan 'yan ta'adda a Ghouta, inda kusan sun kwace iko baki day nakin daga hannun 'yan ta'adda, inda ban da 'yan tsiraru da suka rage da bas u ko kasha biyu cikin dari ba, a lokacin da yankin yake a hannun 'yan ta'ada baki daya sojojin Syria ba su amfani da wadannan makamai ba sai yanzu? Wannan ya saba wa hankali.

Haka nan kuma dalili na biyu shi ne, Syria tana cikin kasashen da suke cikin yarjejeniyar hada yaduwar makamai masu guba, kuma an lalata dukkanin sanadaranta masu guba karkashin kulawar majalisar dinkin dinkin duniya, Amurka da majalisar dinkin duniya sun bayar da rahotoa  rubuce kan cewa gwamnatin Syria bata da makamai masu guba, to yaya ta kai hari da su? Wannan ma abin dubawa ne.

Bayan haka kuma babu wani dalili na bincike da ya tabbatar da haka, bil hasali ma wadanda suka bayar da sheda kan hakan suna tare da kungiyoyin 'yan ta'adda, kuma bisa abin da suka fada ne zaa hukunta gwamnatin Syria, ya ce wannan rashin adalci ne.

3704044

 

 

 

captcha