IQNA

'Yan Ta'adda Sun Kaddamar Da Hari Da Makaman Roka A Damascus Daga Ghouta

23:41 - April 08, 2018
Lambar Labari: 3482551
Bangaren kasa da kasa, Rahotanni daga kasar Syria sun ambato cewa, kimanin mutane 6 suka rasa rayukansu a jiya, biyo bayan harba makaman roka da 'yan ta'adda na kungiyar Jaish Islam suka yi daga unguwar Doma da ke gabashin Ghouta zuwa birnin Damascus.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, sauran 'yan ta'addan kungiyar Jaish Islam da suka ki mika wuya da suka kafa tunga  a unguwar Doma da ke yankin Ghouta a gabashin birnin Damascus na Syria, a jiya sun harba makaman roka da suka sauka  cikin birnin Damascus, tare da kashe fararen hula 6 da kuma jikkata wasu.

Wannan hari na 'yan ta'addan ya zo ne a daidai lokacin da shugabansu Muhammad Allush ke fadar cewa zai tattauna da Rasha kan a ba su damar ficewa daga yankin salun alun, kamar yadda ita gwamnatin Saudiyya wadda ta kafa wannan kungiya ta Jaish Islam kuma take daukar nauyinta take kokarin ganin an bar 'yan ta'addan sun fice daga yankin na Doma.

Wasu rahotannin na daban sun tabbatar da cewa, bayan harba makaman roka kan birnin Damscus, 'yan ta'addan na kungiyar Jaish Islam sun harba wasu makamai masu guba a wasu bangarori na unguwar ta Doma, da nufin dora alhakin hakan kan sojojin kasar Syria, domin dauke hankulan al'ummomin duniya kan ta'asar da suke tafkawa.

3703517

 

 

 

captcha