IQNA

An Yi Wa Wani Fitaccen Malamin Addinin Muslunci Kisan Gilla A Yemen

23:55 - April 09, 2018
Lambar Labari: 3482554
Bangaren kasa da kasa, wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun harbe Sheikh Salama kasiri wani babban malmin addini a garin Siun na Hadra Maut a Yemen.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, shafin yada labarai na yamniat ya habarta cewa, a yau Litinin wasu mutane dauke da makamai sun harbe Sheikh Salama Kasiri wani babban malmin addinin musulunci kuma malamin darikar sufaye a garin Siun na Hadra Maut na kasar Yemen.

Ko a shekarar da ta gabata ma wasu mutane da ba a san ko su wane ne sun harbe wani babban malamin addinin muslunci Sheikh Rus Bin Sumait a garim Turaim da ke cikin gundumar ta hadra Maut.

Gundumar Hadra Maut dai tana a karkashin ikon dakarun da ke biyayya ga shugaban kasar Yemen da ya yi ritaya kuma ya tsere Hadi Mansur, kuma suna kai ruwa rana da masu biyayya ga hadaddiyar daular larabawa.

Haka nan kuma yankin na Hadra Maut na dadden tarihi a cikin addinin muslunci, inda aka yi malamai da dama da suka yi rubuce-rubuce na addini.

3704323

 

 

 

 

captcha