IQNA

Zaman Gaggawa Na Kwamitin Tsaron MDD Kan Harin Da Aka Kai Syria

23:44 - April 14, 2018
Lambar Labari: 3482568
Bangaren kasa da kasa, Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar da zaman gaggawa a yau, domin tattauna harin da kasashen Amurka da Birtaniya gami da Faransa suka kaddamar a kan Syria.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Zaman tarin kwamitin tsaron dai ya zo ne bayan da Rasha mamba ta din-din-din a kwamitin ta bukaci hakan, inda jakadan Rasha majalisar dinkin duniya ya yi tir da Allawadai da kakkausar murya kan harin, yayin da jakadun murka, Birtaniya da Faransa suka kare kasashensu kan wannan mataki.

A nasa bangaren babban sakataren majalisar dinkin dinkin duniya Antonio Guterres ya nuna damuwarsa matuka kan yadda batun Syria ke neman ya zama wata fitina da za ta shafi duniya baki daya, ya ce dole ne dukkanin mabobin kwamitin tsaro su yi aiki da nauyin da ke kansu na tabbatar da sulhu da zaman lafiya a Syria da duniya baki daya, maimakon azuzuta wutar rikci da zai cutar da al'ummomi a duniya.

3705518

 

http://iqna.ir/fa/news/3705518

 

 

 

captcha