IQNA

Ethiopia Za Ta Halarci Gasar Kur'ani Ta Duniya A Iran

23:25 - April 18, 2018
Lambar Labari: 3482580
Bangaren kasa da kasa, karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Habasha ya sanar da cewa Abdulmajid Naser mahardacin kur'ani dan kasar ta Habasha zai halarci gasar kur'ani ta Iran.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, karamin ofishin jakadancin Iran a birnin Addis Ababa ya sanar da cewa, Abdulmajid Naser mahardacin kur'ani dan kasar ta Habasha ya kama hanyarsa ta isa Tehran domin halartar gasar kur'ani ta duniya karo na 35 da za a gudanar a kasar Iran.

A gobe ne dai za a bude gasar wadda babban masallacin marigayi Imam Khomenei da ke cikin birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, tare da halartar makaranta da mahardata kur'ani kimanin dari uku da saba'in daga kasashen duniya daban-daban.

3706687

http://iqna.ir/fa/news/3706687

captcha