IQNA

Kungiyar Daesh Ta Dauki Alhakin Harin Afghanistan

23:54 - April 22, 2018
Lambar Labari: 3482595
Bangaren kasa da kasakungiyar 'yan ta'addan daesh ta dauki alhakin harin ta'addancin da aka kai yau a Kabul.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin Alnashrah ya bayar da rahoton cewa, an kai harin ne nay au a lokacin mutane suke cikin layi somin yin rijistar zabe.

Wannan harin dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 37 tare da jikkatar wasu fiye da 50 na daban, kungiyar 'yan ta'adda ta Daesh ta sanar da cewa ita ce ta kai harin saboda abin da ta kira da cewa zabe kafirci ne da shirka.

Tun bayan faruwar lamarin dai jami'an tsaro sun kafa shingaye tare da hana shige da fice a yankin da abin ya faru domin gudanar da bincike.

3707902

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha