Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, shafin yada labarai na Bawwaba Arab ya habarta cewa, an girmama daliban makarantun sakandare da suka gudanar da gasar kur’ani a kasar Qatar a birnin Doha fadar mulkin kasar.
A kowace shekara ana gudanar da gasar kur’ania cikin watan Ramadan mai alfarma ta daliban makarantun sakandare a Qatar.
An gudanar da taron rufe gasar ne a babban dakin taruka na Abdullah Bin Zaid.