IQNA

Gobara A Cibiyar Darul Kur’ani Ta Kirawan

23:52 - June 02, 2018
Lambar Labari: 3482719
Bangaren kasa da kasa, gobara ta kama a babbar cibiyar Darul kur’an da ke birnin Kirawan na kasar Tunisia.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne gobara ta kama a babbar cibiyar Darul kur’an da ke birnin Kirawan na kasar Tunisia amma daga bisani ‘yan kwana-kwana sun samu nasarar kasha gobarar.

Rahoton ya ce gbarar ta yi sanadiyyar konewar wasu daga cikin kayayyakin da suke a cikin cibiyar.

Daga cikin kayan da suka kone har da ittafai da kuma da kuma wasu kayan cibiyar da suka hada da kujeru da kuma dakin daukar shirye-shirye wato studio.

Wannan cibiya dai it ace cibiyar kur’ani mafi girma  akasar Tunisia, kamar yadda kuma tana daga cikin manyan cibiyoyin kur’ani masu tarihi a nahiyar Afirka.

3719864

 

 

 

 

captcha