Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a yau ne za a fara gudanar da gasar hardar kur’ani mai tsarki ta birnin Alkahira da ake gudanarwa a kowace shekara.
Atef Abdulhamid gwamnan Alkahira da kuma Muhamad Sayyid shugaban bangaren kula da harkokin addini na birnin da wasu manyan jami’ai daga ma’aikatu daban-daban duk za su halarci taron bude gasar a daren yau Alhamis.
Muhammad Sayyid ya ce adadin wadanda suka yi rijistar halartar gasa ya kai mahardata 1200.
Ya kara da cewa, za a gudanar da gasar kamar yadda aka saba a dukkanin bangarori na harda, haka nan kuma daga karshe za a bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo.