IQNA

Karshen Gasar Kur’ani A Kasar Aljeriya

23:19 - June 11, 2018
Lambar Labari: 3482749
Bangaren kasa da kasa, a daren yau ne za a rufe gasar kur’ani ta duniya karo na goma sha biyar a kasar Aljeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Sumaih Khalid Ahmad Usamina daya daga cikin manyan alkalan gasar ya bayyana cewa za a rufe gasar  ta duniya karo na goma sha biyar a kasar Aljeriya wadda ta kunshi harda, tajwidi da kuma tafsiri.

Ya ci gaba da cewa dukkanin kasashe 53 da suka halarci gasar sun yi rawar gani, da suka hada da kasashen musulmi da ma wadanda ba na musulmi ba.

A daren yau ne za a sanar da sakamao gasar, inda za a bayar da kyautuka ga dukkanin mahalarta gasar, kamar yadda za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo.

3721788

 

 

 

 

 

captcha