IQNA

Ofishin Ayatollah Sistani Ya Bada Umarnin Dubar Wata Gobe

23:52 - June 13, 2018
Lambar Labari: 3482753
Bangaren kasa da kasa, ofishin babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya bada umarnin duba watan shawwal gobe alhamis a fadin kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Saumaria News ya habarta cewa, ofishin babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya bada umarnin duba watan shawwal gobe alhamis a fadin kasar ta Iraki.

Bayanin ya ce bisa la’akari da cewa ganin wata da idanu kai tsaye gobe a wasu yankuna na kasar Iraki yana da wahala sai dai da na’ura, amma duk da haka an bukaci musulmi da su sanya id gobe domin duba watan.

A wasu kasashe ma tuni aka bukaci jama’a da su duba wata gobe, idan har aka samu bayanin ganin watan a gobe to rana Juma’a za ta zama daya ga watan shawwal, kuma ranar karamar salla.

3722686

 

 

 

 

 

captcha