Uraikat yayi kiran a lokacin da yake zantawa da manzon musamman na kungiyar tarayyar turai, inda ya sheda masa cewa, babban abin dayake gaban tarayyar turai shi ne ta amince da Palestine mai cin gishin kanta da babban birninta quds.
Haka nan kuma yayi wakilin na tarayyar turai bayani kan halin da ke ciki na kisan da Isra’ila take kan palastinwa a cikin lokutan baya-bayan nan.