IQNA

Sallar Idi Tare Da Limancin Jagoran Juyin Musulunci

23:56 - June 15, 2018
Lambar Labari: 3482761
Bangaren syasa, al'ummar Iran kamar sauran mafi yawan al'ummun duniya a yau Juma'a ne suka gudanar da sallar idi karama wata idir fitir karkashin limancin Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran a hubbaren Marigayi Imam Khomeini da ke birnin Tehran.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habata cewa, a khudubarsa ta sallar idi karama a yau Juma'a: Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khameine'i ya jinjinawa al'ummar Iran kan yadda suka fito zanga-zangar ranar qudus ta duniya a karshen juma'ar watan ramadana mai alfarma duk da tsananin zafin rana da ake yi lamarin da ya rusa duk wani makirce-makircen da ake kitsawa na kashe gwiwar al'ummar Iran kan aniyarsu ta goyon bayan al'ummar Palasdinu da kare Masallacin qudus mai alfarma. 

Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci a hudubar tasa a masallacin Imam Khomeni (RA) ya bayyana yadda bakar siyasar amurka take ci gaba da tarwatsewa musamman furucin da shugaban Amurka ya yi na cewa sun kashe biliyoyin kudade na dala a yankin yammacin Asiya amma basu cimma nasarar da suka sanya a gaba ba.

A yau ne mafi yawan kasashen musulmi ciki har da nahiyar Afrika suke gudanar da bukukuwan sallar idir fitir bayan da suka tabbatar da ganin wata a jiya Alhamis. 

3722904

 

 

 

 

captcha