Kamfanin dillancin labaran iqna rahoton ya nakalto cewa a cikin watan Mayu na wannan shekarar kadai an sami wuraren dubu daya da dari biyu da sabain da biyu da aka take hakkin dan adam a cikin kasar.
Rahoton ya kuma ci gaba da cewa; Take hakkin bil'ada da aka tabbatar da faruwarsa ya kunshi kai wa gidajen mutane hari, shari'ar da babu adalci a cikinta, murkushe masu gangamin ruwan sanyi.
Bugu da kari rahoton ya ambaci takurawa mutane masu kai da komowa akan tituna ta hanyar kafa shinge a matsayin wani sashe na take hakkin bil'adama. Har ila yau an zargi maukuntan kasar da hana yin sallar juma'a da kuma azabar da fursunoni.
A cikin wannan shekara ta dubu biyu da sha takwas kadai an yi wa mutane dari bakawai da bakwai shari'ar da babu adalci a cikinta, kamar yadda aka kwacewa mutane dari da talatin da biyar hakkin zama 'yan kasa, kamar yadda rahoton ya ambata.
Tun a watan febrairu na dubu biyu da sha daya ne al'ummar Bahrain suka yunukura da zummar kawo gyara a salon siyasar kasar.