Rahotonin talabijin sun ce wani mai magana da yawun dakarun ya ce; Sojojin na Yemen sun kuma harbo wani sojan Saudiyyar guda da kuma da sansanin soja na al-Rumaih a gundumar jizan da ke kudancin Saudiyya.
A wani gefen, dakarun sa-kai na Ansarullah sun kashe 'yan koren Saudiyya masu yawa a yankin alriyah da ke kusa da babban birnin kasar Sanaa.
Kasar Saudiyya wacce take samun cikakken goyon bayan Amurka ta shelanta yaki akan kasar Yemen a watan Maris na dubu biyu da sha biyar wanda kawo ya zuwa yanzu an kashe fiye da mutane dubu sha biyu da jikkawa wasu dubbai.