Kamfanin dillancin labaran iqna, hukumomin tsaro a Jamhuriya Nijar sun sanar da mutuwar sojojin kasar 10 da kuma batar wasu hudu da kuma uku da suka raunana, bayan wani hari da aka kai masu a yankin Diffa a kusa da tafkin Chadi.
Harin wanda ake danganta wa daga kungiyar Boko haram, an dai kai shi ne a cikin daren ranar Asabar data gabata a kauyen Bla Brin, dake nisan kilomita 40daga birnin N'Guigmi a kusa da yankin tafkin Chadi.
Mayakan sun kuma kone motocin soji masu yawa kafin su arce, kamar yadda kakakin ma'aikatar tsaron kasar, Kanal Toure ya tabbatar wa da kamfanin dilancin labaren.