IQNA

Wasu ‘Yan Majalisar Isra’ila Sun Shiga Masallacin Quds

23:31 - July 09, 2018
Lambar Labari: 3482818
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin ‘yan majalisar haramtacciyar kasar Isra’ila sun kutsa kai a cikin masallacin quds mai alfarma.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wasu daga cikin ‘yan  majalisar haramtacciyar kasar Isra’ila sun kutsa kai a cikin masallacin quds mai alfarma da nufin keta alfarmar wannan wuri mai albarka.

Yahudawan sun shiga cikin masallacin ne tare da kariya daga daruruwan jami’an tsaron Isra’ila.

A cikin ‘yan kawanakin nan dai yahudawa suna yawan shiga cikin wannan masallaci mai alfarma domin tsonakar al’ummar musulmi.

Tun bayan da shugaban Amurka ya ayyana birnin Quds a matsayin babban birnin yahudawan Israila a hukumance, yahudawan suke ta kara cin karensu babau babbaka  a kan musulmi da wurare masu tsarki a wannan birni.

3728765

 

captcha