Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, nan da watanni biyu masu zuwa za a gudanar da taron koli na kwamitin kasashen musulmi karo na ashirin da tara a birnin Alkahira.
M'ikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta sanar da cewa an cimma matsaya kan gudanar da taron a birnin alkahira a cikin watan satumba mai zuwa, wanda zai samu halartar baki daga kasashen musulmi.
Babbar manufar taron dai ita ce bijiro da muhimman lamurra da suke ciwa al'ummar musulmi tuwo a kwarya da kuma gabatar da hanyoyin warware su, ta hanyoyi na ilimi da hankali ba ta hanyar yaki da kashe-kashe ba.
Kimanin kasashe 40 ne dai za su halarci zaman taron, haka nan kuma za a gabatar da shwarwari wadanda za a yi dubia kansu kafin zaman a gaba.