IQNA

Iran Ta Maida Martani Kan Zarge-Zargen NATO

23:41 - July 13, 2018
Lambar Labari: 3482832
Bangaren kasa da kasa, Gwamnatin kasar Iran ta yi watsi da damuwar da shuwagabannin kasashe a kungiyar tsaro ta NATO suka nuna dangane da shirin tsaron kasar a taronsu na ranar Laraban da ta gabata a birnin Brussels na kasar Belgium.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,

kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasimi yana fadar haka a jiya Alhamis. Ya kuma kara da cewa Iran ta yi allawadai da rahoton bayan taro wanda kungiyar ta fitar bayan taron shuwagabannin kasashenta a ranar Laraban da ta gabata, wanda ya nuna cewa shirin makamai masu linzamin kasar da kuma rawan da take takawa a gabas ta tsakiya abin damuwa ne a garesu.

Qasimi ya kara da cewa gwamnatin kasar Iran tana bin duddugin taron a ranar Laraba, kuma ta gano cewa shugaban kasar Iran ne ya takura sauran kasashen wajen daukar wannan matakin.

Kasar Amurka ce dai take bada mafi yawan kudaden da kungiyar take kashewa, don haka ne kuma take amfani da damar wajen tilasta masu ra'ayinta.

Qasima ya kara da cewa kasar Iran ba zata taba dakatar da shiringta na makamai masu linzami ba don da shi take kare diyaucin mutanen kasarta, sannan dangane da shirin na makamashin nucliya kuma hukumar kula da makamashin nukiliya ta wadarta wajen tabbatar da wufintar shirin daga ayyukan soje.

3729511

 

 

 

captcha