Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an kai harin ban din ne a yau Juma'a,a lokacin da jama'a masu tarin yawa suka hadua wani gangamin yakin neman zabe a garin Mastung da ke kusa da birnin Kuita babban birnin lardin Balochestan.
Akalla mutane 85 sun rasa rayukansu, wasu fiye da 150 kuma sun jikkata, daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da wasu fitattun 'yan siyasa na lardin da suka hada da Mir Siraj.
Babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin, amma dai ana nuna yatsan tuhuma a kan kungiyar Taliban da kungiyoyin masu dauke da akidun takfir.